An dage hawan sallah a Katsina

Shugaba Buhari da sarkin Katsina
Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya aike da tawaga don yi wa jama'ar jihar Katsina jaje

Fadar masarautar Katsina ta fitar da wata sanarwar, wadda a ciki ta aike sakon jaje ga daukacin jama'arta kan ibtila'in kashe-kashen da mutanen gundumomin Batsari, da Dan-Musa, da Kankara da Wagini da sauransu wuraren da abun ya shafa suka samu kansu a ciki.

Sakataren masarautar Alhaji Bello M IFO shi ne ya fitar da ita, tare da shaida wa jama'a ce wa sakamakon halin da suka samu kansu a ciki na alhini da jimami, masarautar ta yanke shawarar a wannan karon ba za a yi hawan sallah kamar yadda aka saba ba.

Alhaji Bello ya ce Mai-martaba sarkin Katsina Dr Alhaji Abdulmumin Kabir Usman CFR, da majalisar masarautar ne suka ga dacewar dage duk wasu shagulgula don nuna alhini kan abin da ya samu jama'arsu.

A karshen sanarwar ta ce za a je sallar idi kamar yadda aka saba, da yin addu'o'in neman zaman lafiya ga jihar Katsina da Najeriya baki daya.